Gwamnan Bauchi ya kirkiri sababbin masarautu 13 a jihar

Gwamnan jihar Bauchi,Bala Muhammad ya rattaba hannu kan sabuwar dokar nadi da kuma sauke sarakuna wacce ta bayar da dama ƙirƙirar sababbin masarautu 13 da kuma gundumomi 111 a fadin jihar.

Har ila yau gwamnan ya sanya hannu kan gyaran dokar Masarautar Sayawa inda aka samar da Masarautar Zaar dake da hedkwata a  garin Mhrim Namchi dake karamar hukumar Tafawa Balewa ta jihar.

Masarautun da dokar ta samar sun hada da Masarautar Burra dake da hedkwata  Burra, Masarautar Duguri dake da hedkwata a Yuli, Masarautar Dambam dake da hedkwata a Dambam, Masarautar Bununu dake da hedkwata a Bununu, Masarautar Lere dake da hedkwata a Lere, Masarautar Darazo dake da hedkwata a Darazo, Masarautar Jama’a dake da hedkwata Nabardo.

Sauran sun hada da Masarautar Lame dake da hedkwata a  Gumau, Masarautar Toro dake da  hedkwata a Toro, Masarautar Ari  dake da hedkwata a Gadar Maiwa, Masarautar Warji dake da hedkwata a Katangar Warji, Masarautar Giade dake da hedkwata a Giade da kuma Masarautar Gamawa dake da hedkwata a  Gamawa. Masarautar Sayawa Zaar dake da hedkwata a Mhrim Namchi.

More from this stream

Recomended