
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya amince a ɗauki sabbin ma’aikata 1480 domin cike gurbin da hana ɗaukar ma’aikata da gwamnatin, Barrister Muhammad Abubakar ta saka ya haifar.
Gwamnan Abubakar ya dakatar da daukar ma’aikata domin ya samu damar tantance su domin a cewarsa suna cinye kaso mai tsoka na kuɗin da jihar take samu shima Bala Muhammad ya cigaba da bin wannan tsari a lokacin da yake kokarin raba jihar da ma’aikatan bogi a mulkinsa zango na farko
Biyo bayan rantsar da shi a karo na biyu, Muhammad ya sanar da janye hanin domin cika alkawarin da ya ɗauka ga mutanen jihar a ranar 29 ga watan Mayu.
Shugaban ma’aikatan jihar, Adamu Yahuza shi ne ya sanar da haka ga yan jarida a jiya.
Ya ce 1000 daga cikin ma’aikatan da za a ɗauka za su kasance malaman makaranta.