Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince da fitar da Naira miliyan 10 a matsayin tallafi ga sojojin da suka samu raunuka a Borno.
Hakan ya nuna cewa Gwamna Zulum ya cika alkawarin da ya yi watanni biyu kafin bikin Sallah da Manjo Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan soji ya shirya.
A hedikwatar shiyya ta 7 da ke Maiduguri a ranar Asabar din da ta gabata, Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na Jihar, Farfesa Usman Tar, ya bai wa Manjo Janar Peter Malla, GOC na Runduna ta 7 ta Sojojin Nijeriya, kyautar Gwamnan Jihar tare da Babban Sakatare, Mustapha Busuguma.
Tar ya ce, “Mun zo nan ne domin cika alkawarin da mai girma Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi.
“Za ku iya tuna cewa gwamnan ya zo ne a ranar Sallah domin wani biki, inda ya bayyana kudirin gwamnatin jihar Borno kan jin dadin dakarun mu tare da bayar da gudunmawar N10m ga sojojin da suka jikkata. Da safe ya aike mu mu zo mu kai kyautar.”
Ya kuma yaba wa sojoji kan tabbatar da zaman lafiya a jihar da kuma kare martabar Najeriya.
Yayin da hukumar ta GOC 7 ta karbi kyautar, Malla ya gode wa Gwamna Zulum bisa wannan karimcin.