Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta yi na kama tsohon Gwamnan Jihar, Yahaya Bello a gidansa mai lamba 9, titin Benghazi, Wuse Zone 4, a gidansa da ke Abuja.

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun mamaye titin ne da misalin karfe 9.30 na safiyar ranar Laraba inda suka killace gidan tsohon gwamnan, inda kuma suka hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa.

Jami’an na EFCC dai sun samu tirjiya daga hannun ‘yan sanda sanye fa bakaken kaya.

Dan jarida wanda ya ziyarci gidan a ranar Laraba da yamma, ya lura da yadda jami’an EFCC dauke da muggan makamai, ‘yan sanda, jami’an ma’aikatar harkokin gwamnati, sashin yaki da ta’addanci da kuma jami’an tsaro na sirri suka taru a gidan na Yahaya Bello.

Bello dai yana fuskantar tuhum-tuhume ne saboda zargin cin hanci da rashawa lokacin da uake gwamna a Kogi.

More from this stream

Recomended