Gwamna Akeredolu Na APC Ya Lashe Zaben Ondo

Akeredolu wanda ya yi takara karkashin jam’iyyar APC, ya samu nasarar lashe 15 daga cikin kananan hukumomi 18 da ke jihar wave ke kudu masa yammacin Najeriya.

Gwamnan ya samu kuri’a 292, 830 yayin da abokin hamayyarsa Eyitayo Jegede na jam’iyyar adawa ta PDP ya samu kuri’a 195, 791.

Bayanai sun yi nuni da cewa mataimakin gwamna Agboola Ajayi da ya yi takara karkashin jam’iyyar ZLP ya samu kuri’a 69,127.

Zaben na ranar Asabar ya gudana ne kasa da wata guda bayan wanda aka yi a jihar Edo a kudu maso kudancin Najeriyar, wanda PDP ta lashe.

‘Yan takara 17 ne suka kara a zaben da suka hada da gwamna mai-ci Rotimi Akeredolu na jam’iyyar APC, da EyitayoJegede na Jam’iyyar PDP da kuma Agboola Ajayi na jam’iyyar ZLP da suka kalaubalance shi.

Akwai dai rahotanni da ke nuna cewa wasu jam’iyyu na zargin an tafka magudi a zaben.

A zaben 2016, gwamna Akeredolu na APC da Mr. Ajayi na jam’iyyar Zenith Labour Party, (ZLP) wanda shi ne mataimakin gwamna Akeredolu, sun ka da Mr Jegede na jam’iyyar PDP.

Amma Ajayi, ya raba gari da gwamna Akeredolu inda ya sauya sheka ya koma ZLP a wannan zabe don kalubalantar tsohon maigidansa.

Wannan shi ne karo na biyu da manyan jam’iyyun kasar biyu, wato APC da PDP suke gwada farin jininsu a zaben jihohi wanda wasu masu fashin baki ke cewa zai iya zama manuniya ga abin da zai faru a zaben 2023.

A ranar 19 ga watan Satumba, gwamna mai ci Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP ya lashe zaben jihar ta Edo bayan da ya kada abokin karawarsa Osagie Ize-Iyamu na APC.

More News

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...

Magoya bayan APC da dama sun koma NNPP a Kano

Jam'iyar NNPP ta karɓi magoya bayan jam'iyar APC da dama a jihar Kano. Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdul Salam Gwarzo shi ne ya karɓi...

APC ta dakatar da Ganduje a matakin gunduma

Mambobin jam'iyyar APC a mazabar da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje. ...