
Hakkin mallakar hoto
Twitter/Obaseki
Gwamnan jihar Edo da ke kudancin Najeriya Godwin Obaseki ya koma jam’iyyar PDP.
Gwamna Obaseki ya bayyana shiga jam’iyyar ta PDP ne ranar Juma’a da rana a sakatariyar jam’iyyar da ke Benin, babban birnin jihar, kamar yadda PDP ta wallafa a shafinta na Twitter.
Ya fitar daga jam’iyyar ne kwana kadan bayan ya fice daga jam’iyyar APC wacce a cikinta aka zabe si a karon farko.
A makon da ya wuce ne jam’iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.
Sai dai masu lura da harkokin siyasa na ganin rikicin ubangida da yaronsa da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Adams Oshimohle kuma shugaban APC da kotu ta dakatar ne ya yi sanadin hana shi sake takara.