A ranar Talata 23 ga watan Afrilun 2024 ne shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa kasar Netherlands domin ziyarar aiki.
Shugaban kasar zai kuma halarci taron tattalin arzikin duniya da aka shirya gudanarwa a ranakun 28 zuwa 29 ga watan Afrilu a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Litinin, ya ce, “Bisa goron gayyatar da firaministan kasar Netherlands, Mark Rutte, ya yi masa, shugaba Tinubu zai tattauna da firaministan kasar, tare da yin shawarwari masu zurfi da tarurruka daban-daban tare da Mai Martaba Sarki Willem-Alexander da Sarauniya Maxima ta Masarautar.
“Sarauniyar ita ce mai ba da shawara ta musamman ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, watau UNSGSA.
Shugaban zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami’ai. jami’an gwamnati.