Akalla gidaje 10 ne wuta ta kone bayan da gobara ta tashi sanadiyar faduwar tankar mai a yankin Lampe dake karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun.
Lamarin ta faru ne da misalin karfe 07:00 na safiyar ranar Asabar akan titin Matogun.
Shugaban shiyar Lagos na hukumar bada agajin gaggatawa ta tarayya NEMA, Ibrahim Farinloye ya ce ba a samu a asarar rayuka ba a wutar.





