
An shiga fargaba a yankin Victoria Island dake Lagos bayan da aka samu tashin gobara a reshen bankin Access dake kan titin Adetokumbo Ademola da safiyar ranar Laraba.
Tashin gobar ya jefa tsoro cikin mutanen dake zaune a ginin da kuma ofisoshin dake kusa.
Gobarar ta tashi ne bayan da wata motar mai tazo sauke man diesel a injin bada wutar lantarki dake harabar bankin.
Motar tankar da kuma wata mota dake kusa da ita dukansu sun kone kurmus.
Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas da kuma na wasu bankuna da otal-otal dake wurin su ne suka samu nasarar shawo kan wutar.