Gobara ta kone dakunan ajiyar kayayyaki biyu a Kano

Gobara ta kone wasu dakin ajiye kayayyaki biyu na kamfanin Noble Carpet and Rugs dake kan titin Ibrahim Taiwo Road a Kano.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya ce “Mun samu kira da misalin karfe 6:45 na safe daga wani mai suna Auwalu Aliyu Abubakar kan faruwar lamarin dakunan ajiye kayayyaki biyu sun kone a yayin da daya ya tsira.”

“Amma kuma wasu shaguna dake kusa da wurin ajiyar kayayyakin abin bai shafe su ba. Babu asarar rayuka ko jin raunin.”

Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar ya ce baza a iya tantance irin asarar da aka yi ba.

Ya kara da cewa watakila gobarar bata rasa alaka da wutar lantarki.

More from this stream

Recomended