Gobara ta cinye kasuwa a Anambra

Wutar da ta tashi a daren Laraba a kasuwar katako ta Ogbosisi da ke yankin Onitsha a Jihar Anambra ta kone kaya da dama kurmus.

Wani mai amfani da dandalin X mai suna Omaletocracy ya wallafa bidiyon gobarar tare da rubuta: “Kasuwar Head Bridge Onitsha na ci da wuta 18/12/2024.”

A bidiyon, an ga wasu ‘yan kasuwa na kokarin ceton kayansu yayin da wutar ke ci gaba da ruruwa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Alhamis, kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa ba a rasa rai ba a lokacin da gobarar ta faru.

More from this stream

Recomended