Ginin Bene Mai Hawa Biyu Ya Rufta a Abuja

Wani ginin bene mai hawa biyu dake yankin Kubwa a birnin tarayya Abuja ya rufto da safiyar ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu nasarar ceto mutane biyu daga cikin ɓaraguzan ginin.

Jami’an kai ɗaukin gaggawa da suka fito daga Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da kuma sun garzaya wurin da lamarin ya faru.

Ruftawar ginin na zuwa ne kwana guda bayan da wani ginin bene na wata makaranta a jihar Filato ya rufto inda ya rutsa da mutane sama da 200.

Matsalar ruftawar gini matsala ce da ta yi ƙamari a Najeriya kuma ana alaƙanta haka da rashin ingancin gine-gine da kuma yin gini ba tare da samun izinin hukumomi ba.

More from this stream

Recomended