Gidaje 200 sun lalace sakamakon ambaliyar ruwa a Kaduna

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) ta ce gidajen da basu gaza 200 ne ba ambaliyar ruwa ta lalata a ƙananan hukumomin Zaria da Sabon Gari.

Da yake magana da manema labarai a ranar Litinin, Usman Mazadu sakataren hukumar ya koka kan yadda ake samu ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da ake yi a jihar.

Ya ce ruwan da ake ba ƙakƙautawa ya saka koguna sun cika sun tumbatsa har ta kai suna malala wuraren da suke kusa da su.

Mazadu ya ce gwamnatin jihar da ɗauki matakai da suka haɗa da yashe magudanen ruwa da kuma wayar da kan al’umma domin rage tasirin illar ambaliyar ruwan.

Ya kuma shawarci mutanen dake zaune wuraren da suke gangare inda za a iya fuskantar ambaliyar ruwa da su koma wasu wuraren har sai damuna ta wuce

More from this stream

Recomended