A cigaba da shari’ar zaben gwamnan jihar Kano jami’in jam’iyar APC mai karbar sakamakon zaben gwamnan, Rabiu Sulaiman Bichi ya ce ɗan takarar gwamna a ƙarkashin jam’iyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna bai mika sakon murna ba ga abokin takararsa na jam’iyar NNPP, Engr Abba Kabir Yusuf bayan da aka bayyana sakamakon zaben.
Bichi wanda shi ne sheda na 31 da aka gabatar a gaban kotun sauraren karar zaben gwamnan Kano ya bayyana haka lokacin da yake amsa tambayoyi.
A yayin zaman kotun lauyan masu kara, Ofiong Ofiong (SAN) ya gabatar da sheda na 31 da kuma 32.
Sheda na 31, Rabiu Sulaiman Bichi wanda shi ne jami’in APC mai karbar sakamakon zaben a jawabin da yayi a rubuce ya kuma rantse a ranar 9 ga watan Afirilu ya ce ya mikawa hukumar INEC dukkanin suna yen wakilan jam’iyar.
Ya ce ya halarci taron manema labarai da jam’iyar ta gudanar kuma babu inda ya yaji Gawuna ya taya Abba Kabir Yusuf murna.