Ganduje ya nemi Abba Gida-Gida ya dawo jam’iyar APC

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf wato Abba Gida-Gida da ya bar jam’iyarsa ta NNPP ya dawo jam’iyar APC.

Wannan cigaban da aka samu na zuwa ne kasa da mako biyu bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen da aka yiwa gwamna, Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar.

Da yake magana da manema labarai a Kano bayan ganawar da yayi da Abba Gida-Gida, Ganduje ya ce ƙofar APC a buɗe take ga duk wanda zai shiga cikin jam’iyar.

Shugaban na jam’iyar APC ya yi kira ga ƴaƴan jam’iyar dake jihar da kada su ji bacin rai kan rashin nasarar da suka yi a kotun ƙoli ya ce a matsayinsu na cikakkun ƴan siyasa yakamata su godewa Allah.

More from this stream

Recomended