Gwamna Ganduje ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta kula da iyayen marigayiya Hanifa.
Gwamnan jihar Kano a Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa iyayen Hanifa Abubakar ta’aziyyar rasuwar ‘yarsu wacce malamin makarantarsu ya kashe bayan da ya yi garkuwa da ita.
Kwana 47 bayan sace dalibar tasa ‘yar shekara biyar, jami’an tsaro suka kama Abdulmalik Tanko a lokacin da ya je karbar kudin fansa.
Amma gabanin hakan malamin makarantar ta Noble Kids Academy, ya riga ya kashe Hanifa amma duk da haka yake karbar kudin fansa.
“Mun samu tabbaci daga kotun da ke sauraren karar cewa za a yi adalci.” Ganduje ya ce yayin ziyarar ta’aziyyar kamar yadda Sakataren yada labaransa Abba Anwar ya sanar a ranar Litinin.
Gwamnan ya kuma sha alwashin ba zai bata lokaci ba wajen bin umarnin kotu da zarar an yake hukuncin kisa.
“Duk wanda aka samu da laifi a wannan mummunan aika-aika, zai fuskanci hukuncin kisa ba tare da bata lokaci ba, a matsayinmu na gwamnati, tuni mun riga mun fara bin matakan da suka dace.”
Gwamna Ganduje ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta kula da iyayen marigayiya Hanifa.
Dangane da makarantu masu zaman kansu da aka soke lasisinsu, Ganduje ya ce zai duba lamarin.