Ana fargabar tserewar fursunoni biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye gidan yari a birnin Maiduguri.
Aƙalla fursunoni 200 ake kyautata zaton sun tsere daga gidan yarin.
Kawo yanzu hukumomin basu fito sun musalta ko kuma gazgata rahoton tserewar fursunoni ba.
Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro akan yankin tafkin Chadi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce hukumomin da abun ya shafa sun yi Æ™oÆ™arin É“oye labarin amma wasu majiyoyi da ya tuntuba sun tabbatar da faruwar lamarin.
Birnin na Maiduguri ya fuskanci ambaliyar ruwa da bai taɓa fuskanta ba a cikin shekaru 30 biyo bayan ɓallewar madatsar ruwa ta Alu.
Ambaliyar ruwan ta mamaye unguwanni da dama dake birnin abun da ya tilastawa mutane tserewa daga cikin gidajensu.