Fintiri Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta ayyana Ahmad Fintiri na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar Adamawa da aka kammala.

Kamar yadda Farfesa Mohammed Mele jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan jihar ya sanar, Fintiri wanda shine gwamna mai ci a jihar ya samu kuri’u 430, 861 inda ya doke ‘yar takarar jam’iyyar APc A’isha Binani wacce ta samu 396,788.

More from this stream

Recomended