Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yuni a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah Babba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Oluwatoyin Akinlade, babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida.
Sanarwar ta ce, “Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Laraba 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yuni 2023 a matsayin ranakun hutun jama’a domin tunawa da bikin Eid-el-Kabir na bana tare da taya al’ummar Musulmi a gida da kuma kasashen waje.”
“Muna fatan addu’o’i da sadaukarwa da suka zo tare da wannan gagarumin biki, da kuma sakon Eid-el-Kabir, za su kawo zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a Najeriya.”
Musulmai a fadin duniya na shirin gudanar da Sallar Eid El-Kabir, wanda aka fi sani da Babbar Sallah a Arewacin Najeriya, ranar Laraba.