Wani jirgin saman fasinja ɗauke da mutane 62 ya faɗo a wajen birnin São Paulo dake ƙasar Brazil inda ya kashe dukkanin mutanen dake ciki.
Jirgin na É—auke da fasinjoji 58 da ma’aikata 4 a lokacin da yayi hatsarin a ranar Juma’a kamar yadda sanarwar da kamfanin jiragen saman Voepass ya fitar ta ce.
Wasu hoton bidiyo da suka karaɗe kafafen sadarwar zamani sun nuna jirgin nayin hajijiya a sama kafin ya rikito ƙasa.
Ma’aikatar Civil Defence ta Brazil ta ce jirgin ya rikioto kan gidaje da dama.
Hukumomin sun ce gida É—aya ne ya lalace kuma babu wani migadanci da ya jikkata.
Tuni shugaban Æ™asar Lula da Silva ya aika da saÆ™on ta’aziyarsa ga iyalan mutanen a hatsarin ya rutsa da su.