Farashin litar mai ya koma N617

Farashin litar man fetur ya karu zuwa akalla N617 kan kowace lita

Ziyarar da wakilin jaridar Daily Trust ya kai wani gidan man NNPCL dake Abuja da safiyar ranar Talata ya tabbatar da cewa an ƙara kudin man daga N539 ya zuwa N617 kan kowace lita.

Wani da ya saya man ya ce ” Gaskiya ne yanzu na saya akan N617 kowace lita”

Kawo yanzu babu wani dalili kan musabbabin karuwa farashin sai dai ana ganin baya rasa nasaba da hasashen da dillalan man fetur suka yi cewa farashin kowace lita zai iya komawa N700.

More from this stream

Recomended