Farashin ɗanyen man fetur ya yi kasa a kasuwar duniya

0

Farashin gangar danyen mai ya fado kasa da dala $95 a ranar Talata.

Faduwar tasa na zuwa ne biyo bayan saka ran da ake na dawowa da cigaba da tattaunawa kan yarjejeniyar 2015 kan shirin nukiliyar kasar Iran.

An sayar da kowace ganga ɗaya nau’in Brent wanda shi ne nau’in danyen mai da ake amfani da shi wajen saka farashi, kan dala $95.31 hakan na nufin yayi kasa da $1.3.

Danyen mai nau’in West Texas Intermediate an sayar da shi kan dala 89.51 hakan na nufin yayi kasa da dala $1.51.

Ana sa ran yarjejeniyar za ta share hanya ga kasar Iran ta kara man da take futarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here