EndSARS: Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata – tun daga Lahadi 11 zuwa Asabar 17 ga watan Oktoban 2020.

An soke rundunar SARS a Najeriya, an kuma kafa SWAT

A makon da ya ya gabata ne Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya soke rundunar da ke yaÆ™i da fashi da makami a Najeriya wato SARS.

Ya bayyana hakan ne a wani jawabin kai-tsaye ga manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata. Sai dai kwanaki kaÉ—an bayan soke rundunar ta SARS aka kafa wata mai suna Special Weapons and Tactics.

Tun da farko dai soke rundunar ta SARS ta biyo bayan zanga-zangar da aka shafe kwanaki ana yi a wasu jihohin Najeriya, inda ‘yan Æ™asar ke zargin rundunar da kisa ba bisa Æ™a’ida ba da cin zarafin da saÉ“a Æ™a’idojin aiki.

Amma duk da Æ™irÆ™iro sabuwar Rundunar SWAT da gwamnatin Najeriyar ta yi, ‘yan Æ™asar na ci gaba da gudanar da zanga-zanga suna masu buÆ™atar sauyi a fannoni da dama na gudanar da gwamnatin Æ™asar.

Rotimi Akeredolu na Jam’iyyar APC ya lashe zaÉ“en Ondo

A ranar Lahadi 11 ga wata, hukumar zaÉ“e ta Najeriya INEC ta sanar da Rotimi Akeredolu na Jam’iyyar APC a matsayin É—an takarar da ya lashe zaÉ“en gwamnan Jihar Ondo da aka gudanar ranar Asabar.

Mista Akeredolu ya samu kuri’a 292,830, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Mr Eyitayo Jegede yake biye masa da kuri’a 195,791, sai kuma dan takarar ZLP, Agboola Ajayi, wanda ya samu kuri’a 69,127.

Dukkanin ‘yan takarar uku lauyoyi ne kuma sun fito daga mazaÉ“un sanata uku daban-daban – Akeredolu daga Ondo ta Arewa; Jegede daga Ondo ta Tsakiya da kuma Ajayi daga Ondo ta Kudu.

Mista Akeredolu ne gwamnan da ke kan mulki a jihar tun shekarar 2016.

Matasa É—auke da makamai sun tarwatsa ‘yan zanga-zanga a Abuja

Wasu matasa sun tarwatsa masu zanga-zangar #EndSars a shataletalen Berger da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Hotuna da bidiyo da aka yaÉ—a a shafukan zumunta sun nuna yadda matasan suka É“ullo daga wani wuri daban É—auke da sanduna suna kai wa masu zanga-zangar hari.

Baya ga Abuja, an samu irin waÉ—annan matasan da suka tarwatsa irin wannan zanga-zangar a jihohin Filato da Legas da Edo.

A wani ɓangaren kuma, an tarwatsa zanga-zangar neman daƙile matsalar tsaro a arewacin Najeriya da aka gudanar a Jihar Kano ranar Alhamis.

Wasu tsageru ne rike da sanduna da adduna suka tarwatsa su a daidai titin Kabuga da ke ƙwaryar birnin na Kano tare da kwacen wayoyi.

Ganduje ya dakatar da mai ba shi shawara saboda sukar Buhari

A makon da ya gabata ne Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mataimakinsa na musamman kan kafafen yaÉ—a labarai, Salihu Tanko Yakasai kan wata suka da Salihun ya yi a shafin Twitter ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A wata sanarwa da kwamishinan yaÉ—a labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar a ranar Lahadi, ya ce umarnin na gwamnan zai fara aiki ne nan take.

A saÆ™on da Salihun ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya danganta Shugaban Najeriyar da “mara tausayi”, sai dai sa’o’i kaÉ—an ya goge wani É“angare na saÆ™on da ya wallafa.

Salihu Yakasai na mayar da martani ne game da jan Æ™afar da Buhari ya yi game da kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya ke yi na rushe rundunar SARS ta ‘yan sanda sakamakon zargin cin zarafi da azabtarwa da ake zarginsu da yi.

Tattaunawar Ƙungiyar ASUU da Gwamnatin Najeriya

A ranar Alhamis da ta gabata ne Gwamnatin Najeriya ta tattauna da Æ™ungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i, inda da alama tattaunawar ta yi armashi.

Ana tunanin ɓangarorin biyu sun fahimci juna amma kuma hakan bai sa ɓangaren ƙungiyar malaman ya sanar da janye yakin aikin ba inda ƙungiyar ta sake amincewa su sake zama teburin tattaunawa da gwamnati.

Bayanai sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta amince ta biya ƙungiyar ta ASUU naira biliyan 30.

Sai dai kuma gwamnatin ba dukkanin kuÉ—in za ta bai wa jami’o’in ba, za ta dinga fitar da su ne kaÉ—an-Æ™adan tsakanin watan Mayun 2021 zuwa Fabrairun 2022.

An shafe wata shida É—aliban jami’o’i na zaman gida a Najeriya saboda yajin aikin na ASUU duk da É—age dokar kulle da gwamnati ta yi.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

ÆŠan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...