Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya amince da tsige sarakuna biyu a jihar.
Sarakunan da aka tsige sun haɗa da Mai Martaba Jonathan Paragua Zamuna na masarautar,Piriga da Mai Martaba Genaral Aliyu Ilyah Yamma na masarautar Arak.
Kwamishiniyar ƙananan hukumomi ta jihar, Hajiya Umma Ahmad ita ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
A cewar sanarwar daga ranar Litinin sarakunan sun tashi daga matsayinsu.
Ana zargin Gen.Iliyah Yamma da laifin naɗa dagatai huɗu waɗanda ba sunansu gwamnatin jihar ta amince da su ba da kuma rashin zama a masarautar sa.
Shi kuwa Jonathan Damuna an cire shi ne daga mulki biyo bayan rikici da aka samu a masarautar sa tsakanin al’ummomin Gure da Kitimi dake masarautar ta Piriga dake karamar hukumar Lere.
Har ila sanarwa ta ce an cire dagatan ƙauyukan Aban, Abujan Mada da kuma Anji dake masarautar Arak.
