El-Rufai ya tabbatar da sauke Mai Mala Buni daga shugabanci jam’iyar APC

A yanzu dai za iya cewa ta faru ta kare kan batun waye yake da ikon shugabancin jam’iyar APC bayan da ta tabbata cewa gwamna Mai Mala Buni yayi adabo da kujerarsa ta shugabancin jam’iyar.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-rufa’i shi ne ya bayyana haka a wata ganawa da yayi da gidan talabijin na Channels a cikin shirin Siyasa A Yau.

El-Rufai ya bayyana cewa Buni wanda a yanzu yake kasar Dubai zai dawo Najeriya ne a matsayinsa na gwamna amma ba a shugaban APC ba.

Ya ce shugaban rikon jam’iyar a yanzu gwamnan Niger, Abubakar Sani Bello ya samu goyon bayan gwamnoni 19 da kuma shugaban kasa, Muhammad Buhari

More from this stream

Recomended