Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya sake ganawa da wani jigon jam’iyar SDP inda hakan ya ƙara ruruta raɗe-raɗin da ake na tsara makomarsa nan gaba a siyasa.
An nuna hoton El-Rufai a Abuja gidan Sanata Abubakar Gada tare da shugaban jam’iyar SDP na ƙasa, Shehu Gabam tare da wasu jagororin jam’iyar.
Karin waɗanda suke a wurin sun haɗa da Teslim Folarin wanda ya yiwa jam’iyar APC takarar gwamna a jihar Oyo a zaɓen 2023 da kuma Sanata Nazif Sulaiman jigo a jam’iyar PDP daga jihar Bauchi.
Taron ganawar na daren ranar Lahadi a gidan Sanata Gada na zuwa ne jim kaɗan bayan da El-Rufai ya gudanar da taron buɗa baki a gidansa dake Abuja da ya samu halartar mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro,Mallam Nuhu Ribadu da sauran wasu jiga-jigan ƴan siyasa.
A makon da ya wuce ne El-Rufai ya ziyarci Gabam a hedkwatar jam’iyar ta SDP.