El-Rufai Ya Musanta Sauya Sheƙa Daga Jam’iyyar APC Zuwa PDP

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya karyata rahotannin da ke cewa ya sauya sheƙa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP).

A wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, El-Rufai ya ce: “Ku yi watsi da waɗannan ƙarerayi da jita-jita marasa tushe game da alaƙar siyasata. Na tura waɗanda suka baza wannan labari ga lauyoyi na don ɗaukar mataki.”

Muradin El-Rufai ya zo ne bayan jita-jitar da ake yadawa cewa tsohon gwamnan na shirin shiga PDP, lamarin da ya musanta a fili tare da yin gargadi kan yada labaran ƙarya.

More from this stream

Recomended