A jiya ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdulfatah Ahmed a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zaune a Ilorin bisa zargin karkatar da wasu makudan kudade har naira biliyan 1.6 mallakar jihar.
Hukumar ta EFCC na binciken tsohon gwamnan ne tare da kwamishinansa na kudi, Mista Demola Banu (wanda ake tuhuma na 2) kan laifukan da suka shafi karkatar da kudade a lokacin mulkinsa tsakanin 2015-2019.
Hukumar ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume 12.
Rundunar shiyar Ilorin na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyace shi a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu domin ci gaba da gudanar da bincike inda aka tsare shi aka kuma kai shi kotu a safiyar Juma’a.