EFCC ta Shiyyar Legas Ta Tsare Jami’anta 10 Saboda Zargin Rashawa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), reshen jihar Legas, ta tsare jami’anta 10 don binciken wasu zarge-zarge da suka shafi aikinsu.

An tsare jami’an ne makon da ya gabata bisa zargin karkatar da wasu kayayyaki da ba a bayyana su ba.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, Dele Oyewale, ya fitar ranar Laraba, ya ce matakin ya zama dole don tsaftace hukumar daga ayyukan da suka saba wa doka da ka’ida.

Har ila yau, hukumar ta sallami jami’anta 27 a shekarar 2024 saboda laifuka daban-daban da suka hada da zamba da rashin bin ka’idojin aiki.

More from this stream

Recomended