EFCC ta kama wasu yan kasar China da suke ƙoƙarin safarar ma’adinai ba tare da izini ba

Jami’an hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati sun samu nasara kama wasu ƴan kasar China su biyu, Wang Jiang da Wang Richard inda ake zarginsu da yunkurin safarar wani ma’adinai ba tare da bin ka’ida ba.

A ranar 3 ga watan Nuwamba ne aka kama Jiang filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Akanu Ibiam dake Enugu.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an kama Jiang ne a wurin da ake binciken jakunkunan matafiya lokacin da aka gano wasu ma’adinai masu daraja  guda uku a lulluɓe a cikin kayansa.

Hukumar ta EFCC ta ce ta kuma kama ƴan Najeriya biyu Donatus Agupusi da Michael Bennett Agu a ofishin hukumar dake shiyar Enugu.

Sai dai hukumar ta gaza yin bayani kan wurin da aka kama Richard.

“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa Agupusi shi ne mamallakin kamfanin gine-gine na Great Wall Construction kuma shi ne ya ɗauki sauran mutanen da ake zargi aiki,” a cewar sanarwar.

“Binciken ya kuma gano cewa Jiang na ƙoƙarin fitar  da ma’adanin daga ƙasar nan ne domin a gudanar da gwaje-gwaje akan su a ƙasar China.”

More from this stream

Recomended