EFCC ta kama wasu masu hada-hadar canjin kuɗaɗe

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta kama wasu mutane 34 da take zargi suna da hannu wajen yiwa darajar takardar kuɗin naira zagon ƙasa.

A wata sanarwa ranar Juma’a hukumar ta ce jami’anta dake sashin yaƙi da cin zarafin kuɗin naira, yawan amfani da dalar Amurka a mu’ammular kasuwanci a cikin gida Najeriya su ne suka samu nasarar kama mutanen.

Hukumar ta EFCC ta ce ta kama mutanen ne a yankin Wuse Zone 4 dake Abuja ranar 26 ga watan Afrilu.

EFCC ta ce nan bada jimawa za a gurfanar da mutanen a gaban kotu.

More from this stream

Recomended