Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, reshen jihar Kaduna, sun kama wani Nuhu Haruna da laifin zambar naira biliyan ɗaya.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawar, a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba ta bayyana cewa kama Haruna ya biyo bayan koke ne da wani da ba a bayyana sunansa ba ya gabatar a watan Disambar 2023, wanda “an gabatar da wanda ake zargin ne da nufin yin cinikin musayar kudaden waje da ya na N1,020,000.00.”
EFCC ta nuna cewa wanda ya shigar da karar ya ya tura kudin ne a asusun Haruna don samun kwatankwacinsa a dalar Amurka.
Duk da haka, mai shigar da kara “ya bayyana cewa wanda ake zargin ya ba shi shaidar biyan kuɗi wanda ƙarya ne saboda bai ga wannan kudin ba.”
Sanarwar ta kara da cewa “Bincike na farko ya nuna cewa Haruna, wanda ya yi ikirarin cewa shi direba n jirgin sama ne, ya karkatar da kudin ne don amfanin kansa ta hanyar siyan kadarori da ababen hawa da ya yi niyyar amfani da su wajen fara kamfaninsa na Air Unity.