EFCC ta kama masu sayen kuri’a a zaben gwamnan Anambra

Hukumar EFCC dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati tace jami’anta sun  kama wasu mutane uku da ake zargi da sayen kuri’a a zaben gwamnan jihar Anambra da aka yi a ranar Asabar.

A wata sanarwa da ta watsa ranar Asabar a shafinta na X da aka fi sani da Twitter a baya EFCC  ta ce jami’anta ne dake sanya ido kan yadda zaben yake guda suka kama mutanen a sassan jihar daban-daban.

” Mutanen da aka kama sun hada da Emeka Ilokasia wanda aka kama a mazaba ta 2 a karamar hukumar Njikoka Anambra da Nwachukwu Loretta da aka kama a mazaba ta 2, Awkuzu akwati mai namba OO8 a karamar hukumar Oyo da kuma Emuka Chukwudi da aka kama a kauyen Umunachi karamar hukumar Danukofia,” a cewar sanarwar.

“Dukkanin mutanen an kama su ne a lokacin zaÉ“en gwamnan jihar Anambra na ranar 08 ga watan Nuwamba na shekarar 2025,”

Hukumar ta kara da cewa za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

More from this stream

Recomended