Hukumar EFCC ta gayyaci, Betta Edu ministar ma’aikatar jin ƙai da kuma yaki da talauci ya zuwa ofishinta domin gudanar da bincike.
Wata majiya dake hukumar ta EFCC ta bayyanawa jaridar The Cable cewa an gayyaci Edu ta bayyana a hukumar da zarar ta samu dama.
“Gwamnati ta umarce mu da mu bincike ta kan badakalar miliyan 585 kuma za muyi haka,” a cewar majiyar.
Tun da farko a ranar Litinin ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bada sanarwar dakatar da ministar daga aiki har sai bayan an kammala bincike kan zargin da ake mata.
Gayyatar da EFCC ke yi wa ministar na zuwa ne kasa da mako guda bayan EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar ma’aikatar ta jin ƙai da yaki da talauci Sadiya Umar Faruq kan zargin badaƙalar biliyan 37.