Eden Hazard: Dan kwallon Belgium na fama da jinya a Spaniya

Ranar Litinin kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana sunayen ‘yan kwallon Real Madrid da za su buga karawa da Valladolid har da Eden Hazard a cikinsu.

Sai kawai aka sanar da cewar dan kwallon tawagar Belgium ya ji raunin da ba zai buga wasan da Madrid za ta yi ranar Laraba ba.

Kuma sabon ciwo na daban dan kwallon ya ji da zai yi jinyar mako uku zuwa hudu kafin ya dawo taka leda.

Kawo yanzu bai buga wasa ko daya a kakar 2020-21 ba, hakan na nufin sai karshen oktoba watakila Hazard ya fara yi wa Real wasan farko.

Sai dai kuma wasu na gani dan ƙwallon na yawan jin rauni a Spaniya fiye da yadda ya taka rawar gani a Chelsea.

Shin me ke faruwa da Hazard ne? Ko dai kungiyar Stamford Bridge ta caka wa Real Madrid dan wasan kan fam miliyan 89?

Ko a bara Real Madrid ta buga wasan Copa del Rey da Sociedad karawar daf da na kusa da na karshe a Santiago Bernabeu, kuma Eden Hazard bai buga wasan ba.

Hazard dan kwallon Belgium ya yi rauni ne ranar 26 ga watan Nuwamba a wasan Champions League da Paris St Germain.

Dan wasan ya ji rauni ne a karon da ya yi da takwaransa na Belgium, Thomas Meunier a wasan da suka tashi 2-2.

Hazard sai da kai 10 ga watan Fabrairun 2020, kafin ya buga wa Real Madrid tamaula.

Real Madrid ta karbo Eden Hazard daga Chelsea kan sama da £150m

Rashin Hazard bai nuna Real Madrid ba, inda ta ci gaba da cin wasanninta har da lashe Spanish Super Cup da ta yi a bana, bayan nasara a kan Atletico Madrid.

Ko da yake wasu lokutan rashin Hazard a wasan Real Madrid ba ya nuna kungiyar, illa dai an sa ran dan kwallon zai haskaka tun komawarsa Santiago Bernabeu daga Chelsea.

Tarihin raunin da Hazard ya yi a Real Madrid da wanda ya yi a Chelsea:

Hazard ya koma Real Madrid daga Chelsea ranar 7 ga watan Yunin 2019 kan fam miliyan 89, inda ya buga wa Real wasa 14 da cin kwallo daya tal, inda dan wasan tawagar Belgium ya ce ita ce kaka mafi muni da ya ci karo da ita, tun lokacin da ya zama kwararren dan kwallo a tarihinsa.

Dan wasan ya koma Chelsea ranar 7 ga watan Yunin 2019 kan fam miliyan 32, wanda ya buga gasar Lik 222 ya kuma ci kwallo 85, banda sauran wasannin kungiyar.

Ya kuma fara kwallo a kwararren dan wasa a Lile daga 1 ga Satumbar 2007, a kungiyar da ya buga wa wasannin lik 114 ya ci kwallo 36.

Rabonda Hazard ya buga wa Real wasa tun 7 ga watan Agustan 2019 a karawar da Manchester City ta doke Madrid 2-1 a Champions League.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...