Duk wanda ya ce Najeriya kalau ta ke to a binciki kansa-Obasanjo

0

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai matakin da yakamata ace ta kai ba a yanzu.

A cewar Obasanjo duk wanda ya ce komai na tafiya dai-dai a yanzu to yakamata a binciki kansa.

Obasanjo ya fadi haka ne ranar Laraba a wurin taron lakcar Gidauniyar Wilson Badejo karo na 15 a birnin Lagos.

“Nigeria ba ta kai inda yakamata ace ta kai a yanzu ba. Idan wani ya ce dai-dai ne a inda muke yanzu to kan sa na bukatar a duba shi” tsohon shugaban ƙasar ya ce.

A cewar Obasanjo dole ne yan Najeriya su zabi ɗan takara na gari a 2023 saboda cigaban kasar na tsaka mai wuya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here