HomeMoreDubban masu zanga-zanga a Israi'la sun bukaci Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya...

Dubban masu zanga-zanga a Israi’la sun bukaci Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya sauka

Published on

spot_img
Jama'a da dama a Israi'la na cikin wahala saboda matsalar tattalin arziki

Bayanan hoto,
Jama’a da dama a Israi’la na cikin wahala saboda matsalar tattalin arziki

Dubban ‘yan Israi’la sun gudanar da zanga-zanga a Tel Aviv, don nuna adawa da abinda suka kira kangin tattalin arziki da salon gwamnati na ‘yaki da annobar korona ‘ya tsunduma al’umma ciki.

Matasa da dama sun cika dandalin taro na Robin Square makil sanye da takunkumi, sai dai ba tare da bayar da tazara ba.

A birnin Kudus kuwa daruruwan mutane sun taru a kofar gidan Frai minista Benjamin Netanyahu, suna masu kiran ya sauka daga kan kujerarsa.

‘Yan sanda sun ‘yi amfani da barkonon tsohuwa da ruwan zafi, domin tarwatsa dubunnan masu zanga-zangar, abin da ‘ya rikide ‘ya koma tashin hankali.

Jama’ar na kuma nuna damuwa a kan yadda diyyar da gwamnati ke bayarwa ba ta isa garesu a kan lokaci.

Kananan yan kasuwa da ma’aikata masu zaman kansu da fitattun taurari ne suka shirya zanga-zangar, da ta samu tabarrakin jama’ar gari.

Mutane da dama a kasar sun tagayyara, kuma suna nuna takaici a kan yadda dokokin da aka kafa na ‘yaki da cutar ta korona a kasar ke cigaba da janyo musu wahala.

Bayanan hoto,
Masu zanga-zangar na cewa diyyar da gwamnati ke ba su ba ta isa wajensu a kan lokaci

Yayin da ma’aikatan gwamnati ke samun tallafi, su kuwa ma’aikata masu zaman kansu cewa suke har yanzu ba a cika musu alkawarin basu tallafin da aka musu ba.

Ranar Jumma’ar da ta gabata dai Frai ministan kasar Benyamin Netanyahu ‘ya gana da ‘yan gwagwarmaya domin tattauna matsalolinsu.

‘Ya shaida musu cewa gwamnatinsa, za ta ci gaba da kokarin biyan bukatun Jama’a, da suka hadar da biyansu alkawuran da aka musu na jin kai.

Tun a tsakiyar watan Maris ne hukumomi a Israila suka kakaba dokar kulle, domin ‘yaki da annobar korona.

Tun daga wancan lokaci zuwa yanzu, alkalumma sun nuna cewa an samu karuwar rashin aiki a kasar da kaso 21.

Latest articles

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar Endbadgovernance sun gana da mataimakin...

More like this

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan fashi guda biyu yayin musayar...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana aniyarsa ta gabatar da buƙatar...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje jihar Borno. Buhari ya kai ziyarar...