DSS za su miƙa Emefiele ga EFCC

Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, na shirin sakin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

A cewar majiyoyin fadar shugaban kasa da ma’aikatar shari’a, za a mika Emefiele a hukumance ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC a yau.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan sakin tsohon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Tun ranar 10 ga watan Yuni ne Emefiele ke hannun hukumar DSS bisa zarginsa da hannu wajen zamba da kuma wasu laifuka da dama.

An gurfanar da shi ne a gaban kotu bisa tuhume-tuhume biyu da ake yi masa kan “mallakar makamai ba bisa ka’ida ba a babbar kotun tarayya da ke Ikoyi kuma an bayar da belinsa a kan Naira miliyan 20.

Alkalin kotun, Nicholas Oweibo, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Emefiele a hannun hukumar kula da gyaran hali ta Najeriya har sai an cika sharuddan belinsa amma hukumar DSS ta dage cewa Emefiele ya koma hannunta, lamarin da ya kai ga gamuwa da juna, tsakanin ‘yan sandan sirri da jami’an gidan yari.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...