DSS ta saki Abdulrasheed Bawa

Hukumar tsaro ta farin kaya watau DSS ta saki tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa, bayan ya shafe kwanaki 134 a hannun ‘yan sandan sirrin.

An tabbatar da cewa an saki Bawa ne daga hedikwatar ‘yan sandan sirri ta kasa, ‘Yellow House,’ da ke Abuja, a daren Laraba.

Hukumar DSS ta kama Bawa tare da tsare shi a ranar 14 ga Yuni, 2023, biyo bayan gayyatar da aka yi masa kan wasu dalilai da ba a bayyana ba, bayan da ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu tun a ranar.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan kama Bawa a ranar 14 ga watan Yuni, 2023, ana tuhumarsa da laifin almundahanar kudi a shekarunsa na aiki a hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

Wasu majiyoyi da suka jiɓinci lamarin sun kuma bayyana cewa tsohon shugaban hukumar ta EFCC ya ƙi daukar hayar lauya duk da cewa an tsare shi.

Da aka tuntubi kakakin hukumar DSS, da na EFCC, Dokta Peter Afunanya da Dele Oyewale da yammacin ranar Laraba, ba su amsa tambayar da aka yi kan sakin Bawa ba.

More News

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Wasu ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karɓar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...