
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta samu nasarar sake kama, Abdulazeez Obadaki wani dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo kuma ɗaya daga cikin daurarrun da suka tsere daga gidan yarin Kuje a shekarar 2022.
Daurarru sama da 800 ne cikin har da wadanda yan kungiyar Boko Haram ne suka tsere daga gidan yarin lokacin da wasu yan bindiga dauke da makamai suka kai farmaki gidan yarin.
Obadaki ne ya shirya kai hari kan wasu bankunan kasuwanci dake gari Uromi na jihar Edo da kuma harin da aka kai Deeper Life College dake garin Okene ta jihar Kogi a shekarar 2022.
Wata majiya dake hukumar ta DSS ta bayyana cewa, Obadaki wanda mamba ne na kungiyar yan ta’adda ta Ansaru an kama shi ne da safiyar ranar Juma’a.
A cikin watan Agusta ne mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya sanar da kama biyu daga cikin wadanda suke jagorantar ƙungiyar ta Ansaru da ake zargi da shirya kai harin gidan yarin na Kuje.

