Dokar wa’azi ce za ta yi wa malamai linzami – Sheikh Daurawa

Sheikh Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce ya kamata gwamnatocin arewacin Najeriya su fito da dokoki dangane da yadda ya kamata malamai na Musulunci da na Kiristanci yin wa’azi.

“Ni da ma ra’ayina tuntuni shi ne mu da muke wa’azi ya kamata a tantance mu shin mai wa’azi ya cancanta kuma yana da ilmi.”

Sheikh Daurawa ya kara da cewa “rashin tantance masu wa’azi ne ya sa ake samun rigingimun da ake ciki yanzu haka, inda za ka samu malami ya shiga gidan rediyo ya bude baki yana ta fadin abin da ya zo bakinsa.

Duk malamin da zai yi wa’azi da zage-zage to ba wa’azi yake ba ya zama dan tasha.”

Ya kamata idan akwai tsari to su kansu kafafen yada labarai za su bi wajen tantance wane malami kafin ma su nemi ya yi wa’azi.”

Sai dai Sheikh Aminu Daurawa ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya ce rashin goyon bayan malamai dangane da wannan batu.

“Na sha yin irin wannan kiraye-kiraye na tsaftace harkar wa’azi amma ban samu goyon bayan malamai ‘yan uwana ba.”

‘Bara ba Musulunci ba ce’

Sheikh Aminu Daurawa ya ce kalmar ‘bara’ wadda ta samo asali daga kalamar Larabaci ‘Albarra’ da ke nufin mika hannu a karbi wani abu ‘ba musulunci ba ne’.

Ya ce idan ba da wani dalili na larura kamar sata ko gobara to shi ne aka yadda mutum zai iya neman taimako. Amma sabanin haka “ba musulunci ba ne.”

To sai dai Sheikh Daurawa ya dora laifin yin bara ga gwamnatoci inda ya ce “gazawar gwamnoni ce ta sa har yanzu ba iya samar da mafita ba dangane da batun yin bara da kuma karatun al’qur’ani.”

Ya kara da cewa ya kamata gwamnatoci su fahimci cewa ” akwai talauci a karkara abin da ke tilasta wa iyaye aikewa da ‘ya’aynsu zuwa birane. Saboda haka kokarin wayar da kai kadai ba zai amfani ba.”

Sheikh Daurawa ya kara da cewa duk da bai goyi bayan kyale jama’a musamman kananan yara su yi bara ba saboda ba musulunci ba ce amma “bai kamata a hana tsarin karatun al’qur’ani ba.”

Mayar da almajirai garuruwansu ba mafita ba ce

Sheikh Aminu Daurawa ya ce ba sa goyon bayan dibar almajirai a mayar da su garuruwansu na asali.

“Gazawar gwamnoni wajen tuntubar malaman addinin musulunci kan yadda ya kamata a zamanantar da tsarin karatun al’qur’ani ne yake kara jefa arewacin Najeriya cikin matsala.”

“An ce yanzu akwai almajirai milyan 9 a arewacin Najeriya, shin wane tanadi aka yi musu? Nawa ake ba su a kason arzikin Najeriya? Ka ga duk ba a ba su komai.”

Sheikh Daurawa ya ce mafita ita ce ” a duba yadda wasu kasashen musulmi ke tafiyar da tsarin karatun kur’ani domin a damfara shi.”

A karshe Daurawa ya ce ya kamata jama’a da gwamnatoci su fahimci banbanci tsakanin bara da karatun allo.

Ba cutar korona na yi ba

Fitaccen malamin ya kuma yi tsokaci kan ‘yar rashin lafiyar da ya yi a ‘yan kwanakin baya abin da ya sa aka daina jin duriyarsa.

“Da ma haka rayuwa take wata rana kana da lafiya wata rana ba ka da lafiya. rayuwa kullum cikin jarrabawa ake.

Hakika na samu jarrabawar rashin lafiya, inda na yi fama da Maleriya da Typhoid da kuma mura mai zafi.”

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...