Barcelona ta gabatar da Dani Alves a matakin sabon dan wasanta ranar Laraba a Camp Nou.
An gabatar da shi a gaban magoya baya 10,000 daga nan kuma ya gana da ‘yan jarida, bayan bikin gabatar da shi da jawabai.
Dan wasan tawagar Brazil zai yi wa Barcelona tamaula a karo na biyu, zai kuma sa riga mai lamba takwas, irin wadda ya yi amfani da ita Sevilla.
Wannan shine karo na biyar da Alves zai saka riga mai lamba daban-daban a kungiyar, bayan da zai buga mata tamaula a karo na biyu.
Daga cikin wadanda suka yi amfani da lamba takwas a Barcelona sun hada da Andres Iniesta da Ludovic Giuly da Hristo Stoichkov da kuma Guillermo Amor da Albert Celades da Phillip Cocu da Arthur Melo da kuma Miralem Pjanic.
Alves ya fara sa riga mai lamba 20 a karon farko da ya je Barcelona a 2008, bayan kaka hudu ya koma saka lamba biyu, sannan ya karbi lamba 22 don girmama abokin taka ledarsa Eric Abidal.
Ya kuma sa riga mai lamba shida, bayan da Xavi Hernandez ya bar Barcelona, wanda yanzu ke horar da kungiyar ta Camp Nou.
Alves ya fara atisaye a Barcelona tun daga Litinin, amma ba zai buga wa kungiyar gasa ba har sai watan Janairun 2022.
(BBC Hausa)