Dan wasan Arsenal Torreira ya karya kafa | Sport News

Arsenal
Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dan wasan Arsenal, Lucas Torreira ya karya kafa a lokacin da yake buga wasan zagaye na biyar da Portsmouth ranar Litinin.

Torreira, mai shekara 24, sai cire shi aka yi daga fili a minti na 16, sakamakon ketar da dan wasan Portsmouth, mai tsaron baya James Bolton ya yi masa.
Har yanzu ba a san ranar da zai dawo filin tamaula ba, domin Arsenal na jiran likitoci su fayyace lokacin da zai gama jinya.
Torreira ya buga wa Gunners wasa 33 a kakar bana.
Sai dai kuma Kieran Tierney ya koma atisaye, bayan rauni da ya yi a kafada.
Yin jinya ya kawo wa Tierney tsaiko a Arsenal wadda ya yi wa karawa 11 tun komawarsa kungiyar farkon kakar nan.
Arsenal na fatan Cedric Soares zai koma yin atisaye a makon gobe, bayan jinyar ciwon gwiwar kafa da ya yi, sannan ta na sa ran Sead Kolasinac zai dawo wasa a karshen watan nan.

More from this stream

Recomended