Dan kwallon na farko ya kamu da Coronavirus | BBC Hausa

@

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An killace dan wasan, mai shekara 22, bayan an gano yana dauke da cutar Coronavirus

Wani dan kwallon Italiya dan asalin Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus.

King Paul Akpan Udoh da ke wasa a kulob din Pianese a gasar Serie C, shi ne kwararren dan kwallon kafa na farko da ya kamu da cutar.

An killace dan wasan, mai shekara 22, bayan an gano yana dauke da cutar mai shafar numfashi ne a ranar Alhamis.

King Paul ya taba buga wa kungiyar Juventus wasa kafin ya koma gasar Serie C, da ke mataki na uku.

‘Yan kwallon da suka damu game da yaduwar Coronavirus sun fara tuntubar hukumomi “saboda da tsoron” ana iya tilasta musu yin wasa a ”wurare masu hadari sosar”, in ji hukumar Fifpro.

A cikin sanarwar da ta fitar, Fifpro ta ce a akwai barazanar harkokin kwallon kafa na iya zama “hanyar yada” cutar.

”Tattaunawarmu da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa ta duba yiwuwar sauya ranakun wasannin kasa da kasa, ciki har da na neman samun gurbi a gasar Olympic da ta cin Kofin Duniya,” in ji hukumar.

Tuni aka dage ranakun wasannin gasar Zakarun nahiyar Asiya ta AFC na mako mai zuwa, sakamakon yaduwar cutar.

More from this stream

Recomended