Wani dan Kano mai suna Suleiman Isah da ya auri wata Ba’amurkiya Janine Reimann ya shiga aikin sojan Amurka.
A ranar 13 ga Disamba, 2020, Mista Isah, wanda a lokacin yana da shekaru 23, ya auri Ms Reiman, mai shekaru 46.
An bayar da rahoton cewa, masoyan biyu sun hadu ne a dandalin sada zumunta na Instagram watanni 10 kafin aurensu.
Labarin shigar wannan matashi aikin sojan ya karaɗe dandalin sada zumunta sosai saboda yadda yin farko al’amarinsa ya shahara.
