Dalilin ‘yan sanda na gayyatar shugabannin al’umma daga Filato

IGP Mohammed Adamu

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Police Force

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta tabbatar da gayyatar wasu shugabannin al’umma da shugabannin Fulani makiyaya wadanda suka fito daga yankunan kananan hukumomin Mangu da Bokkos da Barikin Ladi da kuma Riyom.

Rundunar ‘yan sandan wadda ta tabbatar wa BBC hakan, ta ce ta gayyace su ne don su amsa wasu tambayoyi dangane da rikicin da ya dabaibaye yankunan kananan hukumomin hudu, to sai dai daga bisani an tisa keyarsu zuwa hedikwatar ‘yan sandan kasar.

Tun da farko dai rikici ne ya barke a wata mashaya a kauyen Kwatas da ke karamar hukumar Bokkos lamarin da ya kai ga harba bindiga a wurin.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum 13 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka rasa ransu.

Bayanai na cewa rikicin ya watsu zuwa kananan hukumomin Mangu da Barikin Ladi da kuma Riyom bayan da wasu suka kaddamar da harin ramuwar gayya kan Fulani makiyaya.

Gwamanan jihar Filato Simon Bako Lalong a ranar da lamarin ya afku yayin wani taro da shugabannin al’umma da jami’an tsaro, ya umarci a kama duk shugabannin yankin.

To sai dai al’ummar Fulani na kokawa da cewa an kama mutanensu da yawa.

Mista Dan Manjang shi ne kwamishinan watsa labarai da sadarwa na jihar, ya kuma shaida wa BBC cewa “An gayyaci shugabannin al’umma da dattawa zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jiha, kuma da kansu suka zo.

“Sarakunan gargajiya na wajen kimanin 11 da aka yi wa tambayoyi, kuma wadanda aka ga suna da matsala, sai aka tafi da su Abuja bisa umarnin babban sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, don a zurfafa bincike.

“A yau (Alhamis) da safe ne aka kai su Abuja. Iya abin da muka sani kenan kan wannan lamari a halin yanzu,” in ji Mista Manjang.

To sai dai sabanin yadda rahotannin ke nuna cewa shugabannin al’umma da shugabannin Fulani na yankunan da rikicin ya afku an kama su, bayan da gwamanan jihar Filato Simon Bako Lalong ya bai wa kwamishinan ‘yan sandan jihar umarni, ASP Uba Gabriel wadda shi ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da cewa gayyatar su suka yi.

Alhaji Isa Baffa shugaban kungiyar Fulani makiyaya na jihar ya ce ba wai kama ‘yan uwansu Fulani ne ya dame su ba, adalci suke bukata, kuma a kama duk shugabannin kowanne bangare ba wai iya Fulani kadai ba cewarsa.

Haka kuma ASP Uba Gabriel kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato ya tabbatar da cewa zuwa yanzu mutum 11 suka mika hedikwatarsu da ke Abuja don gudanar da bincike.

Jihar Filato dai ta sha fama da rikice-rikicen da ke da nasaba da addini da kabilanci a ‘yan shekarun nan, wadanda suka janyo mutuwar daruruwan jama’a da kuma asarar dukiyoyi.

More News

DA ÆŠUMI-ÆŠUMI: DSS sun cafke Sowore a filin jirgin na Legas

Jami'an Hukumar Ƴansandan Farin-kaya ta DSS sun kama Omoyele Sowore, jagoran kungiyar  #RevolutionNow Movement da ke adawa da gwamnati a filin jirgin sama na...

Ƴan bindiga sun Æ™one ginin hedkwatar Æ™aramar hukuma tare da kashe jami’an tsaro

Ƴan bindiga sun kai farmaki hedkwatar ƙaramar hukumar, Isiala Mbano dake jihar Imo da tsakar daren ranar 3 ga watan Satumba inda suka ƙone...

An kama wasu Æ´anta’adda da ke da alaÆ™a da Turji

Akalla mayaka 18 da ke da alaka da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji aka kama a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin...

Dakarun Najeriya sun kai farmaki wa Æ´an’adda a Borno, wani kwamanda ya miÆ™a wuya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Lahadin cewa dakarunta sun yi nasarar kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar Boko Haram, Abu Rijab da wasu...