Dalilin da ya sa ba abiya ma’aikatan gwamnatin tarayya albashi ba


Wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya da dama na cigaba da nuna rashin jin dadinsu kan yadda har yanzu ba a biya su albashin wata Yuni ba.

Ma’aikatan da dama sun bayyana cewa a yanzu yadda rayuwa ta yi tsada sun fada cikin mawuyacin hali a sanadiyar rashin biyan albashin.

“Ina rokon gwamnatin tarayya ta biya saboda na sayi kayayyakin amfani yarana suna gida suna kuka” a cewar wata ma’aikaciya.

Ana ta bangaren gwamnatin tarayya ta ɗora alhakin matsalar kan tangarda da aka samu a manhajar biyan kudi ta bai daya da take amfani da ita.

Bawa Mokwa, daraktan yaɗa labarai a ofishin akanta janar na kasa shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba.

Ya ce gwamnatin na yin duk mai yiyuwa wajen ganin an warware matsalar.

More from this stream

Recomended