Dalilin da ya sa ba abiya ma’aikatan gwamnatin tarayya albashi ba


Wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya da dama na cigaba da nuna rashin jin dadinsu kan yadda har yanzu ba a biya su albashin wata Yuni ba.

Ma’aikatan da dama sun bayyana cewa a yanzu yadda rayuwa ta yi tsada sun fada cikin mawuyacin hali a sanadiyar rashin biyan albashin.

“Ina rokon gwamnatin tarayya ta biya saboda na sayi kayayyakin amfani yarana suna gida suna kuka” a cewar wata ma’aikaciya.

Ana ta bangaren gwamnatin tarayya ta É—ora alhakin matsalar kan tangarda da aka samu a manhajar biyan kudi ta bai daya da take amfani da ita.

Bawa Mokwa, daraktan yaÉ—a labarai a ofishin akanta janar na kasa shi ne ya bayyana haka a ranar Laraba.

Ya ce gwamnatin na yin duk mai yiyuwa wajen ganin an warware matsalar.

More News

Tinibu ya aikawa da majalisar dattawa sunaye 7 na  ministocin da zai naÉ—a

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga majalisar dattawa da ta tabbatar da sunayen mutane 7 da ya tura majalisar da zai...

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...