‘Dalilan gwamnatoci na ɓoye kayan tallafi ihu ne bayan hari’ – Comrade Kabiru Sa’idu Dakata.
A Najeriya, hukumomi a jihar Filato sun ce sun kama mutum sama da 200 bisa zarginsu da hannu wajen aukawa suto suton gwamnati su ka wawashe abinci.
Ba a jihar Filato ba kadai, lamarin ya faru a wasu jihohin Adamawa da Kaduna da Taraba da Abuja da Cross River da kuma Kwara.
A jihohin ƙasar da dama al’umma sun wayi garin yau cikin dokar hana fita da hukumomi suka ƙaƙaba ta tsawon sa’a 24, bayan zanga-zangar nuna adawa da rundunar ‘yan sanda SARS ta rikiɗe zuwa tarzoma.