Dalilan da ke sa wasu ke kallon bidiyon batsa a bainar jama’a—BBC Hausa

Asalin hoton, Emma Hermansson

Bayanan hoto,
An ba wa BBC wannan hoton na wani mutum da ke kallon batsa a cikin motar bas ta haya

Bronwen Reed na zaune a ɗakin karatu, tana tsammanin za ta yi karatu kamar kowane ɗalibi, kawai sai ta ga wani mutum yana kallon fim ɗin batsa a kwamfutar ɗakin karatun.

“Na yi mamaki kuma na ji wani yam. Ban san me ya kamata na yi ba a lkacin,” kamar yadda ta shaida wa BBC.

‘Yar shekara 21 ɗin wadda mazauniyar Manchester ce a Ingila, ta zaci abu ne da zai faru sau ɗaya, amma ‘yan makonni sai ta sake ganin irin wannan abin a ɗakin karatun daga mutumin.

A kwanan nan, wani ɗan majalisa na jam’iyyar Conservative a Birtaniya ya saka daga muƙaminsa bayan ya amsa lafiin cewa ya kalli bidiyon batsa a wayarsa yayin da ake zaman majalisar.

Ya faɗa wa BBC cewa lamarin tsautsayi ne saboda yana neman wani shafin motocin tarakta ne, ba wai yana neman shafin batsar ba ne.

A cewar wasu bayanai daga hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Birtaniya, Ofcom, rabin mutane baligai a Birtaniya na kallon fina-finan batsa.

Don gano dalilin da ya sa mutane ke kallon batsa a bainar jama’a da kuma ɓoye, mun tattauna da Dr Paula Hall, wani ƙwararre kan ƙwaƙwalwa da ya ƙware kan waɗanda suka jarabtu da jima’i da kallon batsa a Cibiyar Laurel.

Jarabtuwa

Wani dalili da Dr Hall ta faɗa kuma wanda take yawan cin karo da shi a ayyukanta shi ne yadda kallon bidiyon batsa ke zamar wa mutane jaraba.

“Mun san cewa idan mutane suka jarabtu da wani abu, hanyoyin katangewa suna daina aiki,” a cewarta.

Ko jarabtuwa da giya, ko caca, “hanyoyin dakatarwa na rage aiki”.

Asalin hoton, Bronwen Reed

Bayanan hoto,
“Kawai dai bai dace ba kwatakwata a ɗakin karatu na al’umma, musamman wurin da yara da iyalai ke zuwa,” in ji Bronwen

Ta yi bayani cewa “sha’awa da kuma zaƙuwar kallon fim ɗin batsa” ta fi ƙarfin a bayyana ta da baki: “a’a, sai nan gaba idan na koma gida”.

Idan mutum ya jarabtu, ɓangaren ƙwaƙwalwarsa da ke yin tunani zai fara disashewa.

Wayewa da kuma sauran jama’ar gari

Shi kuwa Callum Singleton na kan hanyarsa ta zuwa Glasgow a bas lokacin da ya ga wani mutum “na latsa wayarsa a bidiyon batsa”.

Abin da ɗan shekara 19 ɗin da farko shi ne “nuna ɓacin rai da kiɗimewa” saboda ya kasa gane me ya sa mutum zai yi hakan a bainar jama’a.

“Da alama abin na neman ya zama ruwan-dare…ya zama rayuwarus ta kullum. Bai kamata kwatakwata,” in ji Callum.

Dr Hall na ganin mutanen da ke kallon a fili “ba su da wayewa ta ƙashin kai”.

“Cikin minti ɗaya suna duba Facebook ko eBay, nan gaba kaɗan kuma sai su shiga wani adireshi da zai kai su fim ɗin batsa.”

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,
Dr Hall ta ce abin kunya ne mai girman gaske

Ta ƙara da cewa “sabar wa mutane” da kallon batsa a bainar jama’a zai iya yi wa al’umma tasiri.

“Kallon batsa ya zama ruwan-dare yanzu” idan aka kwatanta da shekarun da suka wuce kuma bambanci tsakanin abin da ya dace da akasin haka na sake disashewa.

“Idan wasu mutanen na kallon batsa ƙila suna tunannin dukkan mutane da suke kusa a su ma kallo suke. Abin sai ƙara sabawa da shi ake yi.”

Dr Hall na ganin wasu mazan kuma suna tunanin cewa kallon batsa a fili “kamar wani ƙarfin iko ne”.

“Akwai wani abu mai kama da tsanar jinsin mata a harkar nan, cewa ‘ina da ‘yancin kallo'”, a cewarta. Ta ƙara da cewa suna tunanin ba matsalarsu a ce “idan ma wani bai ji daɗi ba”.

Wata ɗabi’a

Idan mutum ya fara kallon batsa yana yaro, zai iya yin tasiri, a cewar Dr Hall.

“Kusan dukkan ayyukan da muke yi indai mun fara su muna yara to yana da muhimmanci sosai game da yadda yake yi mana tasiri kai-tsaye.”

Kuma abu ne mai wuyar gaske “daina wannan ɗabi’ar idan mutum bai fahimci cewa ta zama ɗabi’a ba”.

“Idan har suka saba kallo a irin wannan ƙananan shekarun, to zai zama ɗabi’ar kai-tsaye.”

Bronwen ta ce lamarin “abin damuwa ne sosai” saboda ya kamata wuraren taruwar jama’a su zama na kowa da kowa.

“Ƙarancin wayewar kai abu ne muhimmi da ke taka rawa kan hakan, da kuma ƙila tunanin halin rashin jin daɗin da mutane ke shiga.

“Sukan manta cewa wasu mutanen suna ɗaukar sa a matsayin laifi.”

Related Articles